Limamin Masallacin Haramayn Na Makka Ya Yabawa Gwamna Ganduje Kan Hidimtawa Musulunci

0
1

Daga Muhammad Kabir Kano

Babban limamin Masallacin Haramayn na Birnin Makkah Mai Tsarki kuma shugaban Cibiyar Nazarin Larabci na Jami’ar Ummul Qura, Farfesa Hassan Ibn AbdulHamid Al-Bukhari ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa hidimtawa Musulunci da ya ke yi tare da gwamnatinsa.

Ibn Abdulhamid ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya jagoranci tawagar wasu mashahuran malaman Jami’ar Ummul Qura, zuwa ga fadar gwamnatin Jihar Kano, ranar Litinin, don sanar da Gwamnan abinda ya kawo su Jihar, bisa gayyatar Jami’ar Bayero ta Kano.

“Alhamdulillah tun mu na can mu na samun labaran aikhairin da gwamnatin ka ke yi wajen tallafawa cigaban Addinin Musulunci. Mun yi murna matuka da wannan labari da muke samu. Kuma mun zo mun gani ma da idonmu,” ya ce.

Ya ƙara yabawa yadda Ganduje ya ke abubuwa saboda ci gaban al’ummarsa, sa’annan nan ya tabbatar da cewa kullum a shirye su ke da su tallafawa jihar ta Kano.

Haka-zalika tawogar ta zo Kano ne bisa gayyatar Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) kan wata horaswa ta musamman da za su yi ga alkalai da kuma daliban ilimi, inda wannan ce l horaswa irin ta ta hudu da su ka yi a ƙasar nan.

A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya bayyana yadda dangantaka ta jima tsakanin Jihar Kano da kasar Sa’udiyya tun shekaru da yawan gaske da su ka wuce.

Ya ce “irin wannan dangantaka ce dadaddiya kuma mai inganci tsakaninmu, ta sa har Kasar ta Sa’udiyya ta bude wani ofishin jakadanci a nan Kano. Wanda duk wata alakarmu da wannan ƙasa mai tsarki ta Sa’udiyya ta nan ne mu ke farawa.”

“Alhamdulillah mu na da wani shirin na musamman dama da kasar Sa’udiyya wanda mu ke tura Malamai a na yi musu bita ta sati biyu ko uku. Daga baya bayan nan mun tura mata guda 100 domin su ma su amfana da irin wannan horaswa. Matan kuma Malamai ne na makarantun Islamiyya,” in ji Gwamnan.

Nan gaba kuma za a kara tura mutane wajen irin wannan horaswa. Kamar yadda ya bayyanawa wadannan manyan baki.

Cikin farinciki da walwala ya yi bayanin yadda Gidauniyarsa ta Ganduje Foundation ta ke yin kokarin gaske wajen hidimtawa Musulunci.

Kamar yadda ya ce “Wannan Gidauniya ni ne da kai na nake daukar nauyin dun aikace aikacen da a ke yi. An musuluntar da mutane sama da Dubu Ashirin (20,000) waɗanda ba su da addini ko daya, sun shiga cikin da’irar Musulunci, Alhamdulillah. Kuma sama da shekaru 30 nake tare da wannan gidauniyar tawa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here