Hukumar Kula da Walwala da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ce ta yiwa maniyyatan da yawan su ya kai 5500 allurar rigakafin korona karo na biyu.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba Muhammad Dambatta ne ya bayyana hakan ranar Litinin, inda ya ce da farko dai hukumar ta karɓi adadin allurarbher 4500, bayan nan kuma ta nemi ƙarin guda dubu ɗaya.
Ɗambatta ya ƙara da cewa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a cikin karamci irin nasa, ya bada umarnin cewa ayi amfani da dukkanin cibiyoyin yin rigakafin da a ka tanada domin yin allurar a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Ɗambatta ya ce bayan waɗannan cibiyoyin, akwai kuma wasu na musamman da aka tanada a asibitin Murtala, asibitin Nassarawa da asibitin Mallam Aminu Kano.
Haka kuma shugaban ya buɗe sabon asibitin da aka gina domin maniyyata, inda ya yi bayanin cewa asibitin wanda aka gina shi da harajin da ake fitarwa na kuɗin Hajji, za a fara amfani da shi ne lokacin jigilar alhazai inda daga bisani kuma a maida shi na amfanin al’umma.
Ya kuma godewa Gwamna Ganduje da Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan a bisa hoɓɓasa da suka yi har aka gina asibitin.