TANA ƘASA TANA DABO: Yau Indonesiya za ta bayyana matsayar ta kan zuwa aikin Hajjin bana

0
389

Ministan Harkokin Addini na Ƙasar Indonesiya, Yaqut Cholil Qoumas, ya ce a yau Alhamis, 3 ga watan Yuni, zai bada sanarwa a hukumance dangane da matsayar ma’aikatarsa kan batun Hajjin 2021. Da ma dai tun farko, an tattauna batun ɗaukar matsayar tare da Hukuma ta VIII ta Majalisar Wakilai ta ƙasar.

A ranar Larabar da ta gabata, Ministan ya faɗa cewa, “Duka mambobin Hukuma ta VIII da ni kaina mun zauna mun tattauna batun hajjin daga farko har ƙarshe. Mun cimma matsaya cewa da yake muna da buƙatar harharɗa wasu anubuwa, da yardar Allah za mu sanar da matsayarmu ya zuwa gobe da rana a Ofishin Harkokin Addinai da ke Thamrin. Don haka a ɗan ƙara haƙuri.”

Kawo yanzu dai Ƙasar Saudiyya ba ta bada tabbacin adadin kason maniyyata ga ƙasashe dangane da hajjin na bana ba, sai dai tuni ma’aikatar shirye-shiryen hajji ta ƙasar ta bada wa’adin kammala shirye-shiryen hajjin gwargwadon tsare-tsarenta.

Kazalika, Minista Yaqut ya ce bai san dalilin da ya sanya har yanzu Saudiyya ta gagara miƙa wa Indonesiya izini ba dangane da hajjin 2021, alhali ta bai wai wasu ƙashe 11 nasu izinin, ciki har da Daulara Larabawa, Amurka, Birtaniya Italiya, Ireland, Japan, Jamus, Fransa, Portugal, Sweden da kuma Switzerland.

Mataimakin Shugaban Hukmar VIII, Ace Hasan Syadzily, ya ce ma’aikatar ta shawarta ba za ta tura maniyyata zuwa hajji ba a wannan shekara.

A cewarsa, “Yadda ba za mu iya ba su (Mamiyyatan Hajji) ƙwarin gwiwa ba haka ma ba za mu iya ba su garanti ba, don haka gara kawai a ɗage tafiyar.”

Ace ya ƙara da cewa, wajibi ne gwammati ta bai wa kula da lafiyar maniyyata muhimmanci da kuma haɗarin da ke tattare da yaɗa cutar korona. Yana mai ra’ayin cewa, maimakon zaman jiran Ƙasar Saudiyya gara su yi abin da ya da kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here