Hukumar Hajji ta Kwara ta ƙaddamar da rigakafin korona karo na biyu ga maniyyata

0
408

A yau Litinin ne Hukumar Hajji ta Kwara ta ƙaddamar da rigakafin korona karo na biyu ga maniyyata Hajjin 2021.

Hajj REPORTERS ta rawaito cewa an fara yin rigakafin ne a yau a harabar hukumar da ke Islamic Village, a unguwar Gerewu, a rukunin gidaje na Adewole kan titin kasuwar Mandate, Ilorin a daidai ƙarfe 10 na safe.

An ƙaddamar da rigakafin ne a kan Shugaban Kwamitin masu-faɗa-aji na hukumar, Dr Abdulkadir Sambo Sambaqi, sai kuma Babban Sakataren hukumar, Barrister Ganiyu Ishola Ahmed.

Da ya ke jawabi bayan an yi masa allurar, Babban Sakataren hukumar, Ahmed yace yin rigakafin an yi shi ne domin a kare maniyyatan jihar, da ma waɗanda ba ƴan jihar ba daga kamuwa da cutar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here