Saudiya za ta bayyana matsaya kan zuwa Hajjin bana nan ba da daɗewa ba

0
391

Nan da ƴan kwanaki kaɗan Saudi Arebiya za ta bada cikakkun bayanai a kan Hajjin bana, yayin da annobar korona ke ci gaba da kawo naƙasu a harkokin yau da kullum a faɗin duniya.

Nan bada daɗewa ba Ministan Lafiya da takwaransa na Hajji za su yi bayani a kan yadda Hajjin bana zai kasance a yanayin matsaloli da annobar korona ta haifar, in ji Ministan Yaɗa Labarai na Saudiyya, Majid Al-Qasabi.

“Canje-canjen da korona ta kawo, rashin cikakkiyar masaniyar irin asarar da annobar ta haifar da kuma ƙarancin rigakafin cutar a kasashe da dama sune suka haifar da ɓata lokaci wajen sanar da shirye-shiryen da aka yi na Hajjin 2021,” in ji Al-Qasabi.

A wani taron manema labarai da gwamnati ta shirya, Al-Qasabi ya bayyana cewa mahukunta na fargabar kar Hajji ya zamto wani gurbi na yaɗuwar cutar korona, shi ya sanya a ke ta taka-tsan-tsan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here