…ana tsammanin farashin zuwa Hajji zai kai Naira miliyan 2.7
Kamfanunuwan harkokin Hajji da Ummara da maniyyata a Nijeriya sun shiga fargaba yayin da kawo yanzu, Saudi Arebiya bata bayyana ko Nijeriya ɗin za ta je aikin Hajjin bana ko ba za ta jeba.
Nijeriya ta tsinci kanta a wannan halin ne, inda Saudiya bata bayyana mata adadin maniyyatan da za su je aikin Hajjin 2021, kwanaki 38 ga Arfa, wacce ake sa ran za ta zo a ranar 18 ko 19 ga watan Yuli.
Jaridar Platforms Africa ta rawaito cewa, ko da Saudiya ta bada damar a je aikin Hajjin na bana, to farashin kujera zai yi tashin gwauron zabi.
Paltforms Afrika ta gano cewa shirun da Saudiya ta yi kan adadin maniyyatan da za su je aikin Hajjin bana, wanda bai taɓa faruwa ba, ya haifar da fargaba ga Kamfanunuwan harkokin Hajji da Ummara da maniyyata a Nijeriya da ma sauran ƙasashen duniya.
Tuni dai Indonesiya, ƙasar da ta fi kowacce yawan musulmai a duniya, ta fasa zuwa Hajjin na bana, inda masu ruwa da tsaki a harkar Hajji ke kira ga Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON da ta yi hakan.
Ɗaya daga cikin masu harkokin Hajji, Alhaji Ahmed Yellow Abubakar ya bayyana cewa ba ya jin Saudiya za ta yi aikin Hajjin bana da ƴan ƙasashen duniya.
Yellow, wanda shine Shugaban kamfanin tafiye-tafiye na Eminasta Travels and Tours, an rawaito cewa ya baiwa NAHCON shawarar da ta soke zuwa aikin Hajjin bana.
Ya ce ” a da, alhazai 4 zuwa 5 ne ke zama a ɗaki ɗaya kowa kan farashin Hajji na Naira miliyan 1.3. Amma a halin yanzu da aka sanya waɗannan dokokin, cewa mutane 2 ne kawai za su zauna a ɗaki, zai yi wuya a ce za su zauna a kan miliyan 1.3, sai ya kai miliyan 2.5 ko 2.7.
“To alhazan da suka yi rijistar su nawa ne za su iya biyan wannan maƙudan kuɗaɗen? Saboda haka a je a dawo dai da wuya Hajjin bana ya yiwu ,” in ji shi.
“Gara kawai a hakura mu fara shirye-shiryen hajjin 2022 kamar yadda sauran ƙasashe suka yi bayan da suka soke zuwa Hajjin na bana”
Ya kuma sake nanatawa cewa NAHCON ta soke Hajjin bana domin maniyyata su san matsayin su.
Binciken da jaridar ta yi ya bayyana cewa kawo yanzu dai Saudiya ba ta sanar da ƙasashen duniya kan adadin maniyyatan da za a bawa kowacce a Hajjin bana ba, kuma gashi saura kwanaki 30 a fara ibadar.