Matawalle ya sake naɗa Sarkin-Pawa a matsayin shugaban hukumar Hajji ta Zamfara

0
5

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sake naɗa Abubakar Sarkin-Pawa Dambo a matsayin Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar.

Naɗin Alhaji Dambo na daga cikin sabbin naɗe-naɗen da gwamnan ya yi a makon jiya bayan ya sauke dukkan masu riƙe da muƙamai na gwamnatin sa.

Sanarwar naɗin ta bayyana ne a Talatar da ta gabata cikin wata sanarwar da ta samu sa hannun muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Kabiru Balarabe, wanda kuma HAJJ REPORTERS ta samu kwafinta.

Alhaji Sarkin-Pawa Dambo shi ne shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Alhazai Musulmi na Jihohi.

Kazalika, sanarwar ta sake nuna naɗin da aka yi wa Sheikh Abubakar Muhammad Sodangi Gusaua a matsayin Sugaban Hukumar Zakka da Taimako na Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here