DA ƊUMI-ƊUMI: Iya mazauna Saudiya ne kawai za su yi aikin Hajjin bana

0
2

Ma’aikatar Harakokin Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta bayyana cewa iya ƴan ƙasa da mazauna Saudiya ne kaɗai za su yi aikin Hajjin bana (2021).

Haramain ta rawaito cewa alhazai dubu sittin (60,000) ne kaɗai, da ƴan ƙasa da baƙi na ƙasashe daban-daban da ke zaune a Saudiyya ɗin, sannan suka yi allurar rigakafin korona karo na ɗaya ko biyu, za su yi aikin Hajjin na bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here