DAGA NACHON

0
283

Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta ce ta samu labarin hana ‘yan wajen ƙasar Saudiyya zuwa hajjin bana da Masarautar Saudiyya ta ɗauka. Hukumar ta ce jami’anta da ke Saudiyyar sun tabbatar mata da wannan mataki da Saudiyya ta ɗauka dangane da hajjin 2021.

Da wannan ne NAHCON ta ce, duk da tana sane da cewa matakin ba zai yi wa ‘yan Nijeriya da sauran maniyyata na sassan duniya daɗi ba, amma cewa sun ɗauki matakin a matsayin ƙaddarar Ubangiji mai ikon sa a yi da hanawa. Tare da kira da a koma a nemi tuba wajen Allah don samun zarafin yin hajji a shekaru masu zuwa.

Cikin sanarwar da ta fitar a Asabar ta hannun Shugabar Sashenta na Hulɗa da Jama’a, Fatima Sanda Usara, NACHON ta ce darasi guda da za a koya daga hana ‘yan ƙetare hajji na shekaru biyun da aka yi shi ne, hadisin nan na Annabi SAW da ya hori musulmi da su yi aikin Hajji a lokacin da suke da zarafi tun kafin zuwan lokacin da za a hana su hakan.

Wani darasin a cewar NACHON, shi ne ƙara tabbatar da cewa lallai zuwa Hajji abu ne da sai wanda Allah Ya nufe shi da zuwa.

Hukumar ta ce tana fata kada ‘yan Nijeriya su zamo masu yanke ƙauna daga rahmar Allah, tana mai cewa “Allah Ya sanya mu cikin zaɓaɓɓunSa waɗanda za su yi Hajji nan gaba.”

Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa ‘yan Nijeriya bisa jajircewar da suka nuna da kuma irin goyon bayan da suka bai wa NACHON game da shirye-shiryen hajjin da aka yi kafin wannan lokaci.

Shugaban ya ce, kamar yadda lamarin ya auku a bara inda wasu maniyyata suka buƙaci a maida musu kuɗaɗensu, masu neman haka ma a bana za a biya musu buƙatarsu ba tare da wani jinkiri ba.

Ya ci gaba da cewa ga masu sha’awar son ci gaba da ajiyar kuɗaɗensu a hannun NACHON, sai su saurari shawarwarin da hukumar za ta bayar.

A ƙarshe, Hassan ya bai wa ɗaukacin masu ruwa da tsaki a masana’antar Hajji tabbacin cewa za a sanar da su matakai na gaba da za a ɗauka bayan hukumar ta kammala tattaunawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here