SOKE HAJJIN BANA: A shirye muke mu biya maniyyata kuɗaɗen su- Hukumar Hajjin Abuja

0
5

Bashir Isa

Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Abuja ta ce ta shirya tsaf don maidawa maniyyata kuɗaɗensu sakamakon soke hajjin bana ga ƙasashen waje da Saudi Arebiya ta yi.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Mai magana da yawun Hukumar, Muhammad Lawal Aliyu, ya ce ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan soke zuwa hajji ga ƙasashen da Gwamnatin Saudiyya ta yi ne.

Aliyu ya ce maniyyata 1964 da suka biya wani kaso don tafiya hajjin na da damar su je su karɓi kuɗaɗensu idan sun so kamar dai yadda Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bada umarni.

Kazalika, jami’in ya ce maniyyatan da ke da ra’ayin barin kuɗaɗen su a hannun hukumar don hajjin baɗi, suna da damar yin hakan don ba su damar zama daga cikin ‘yan sahun gaba da hukumar za ta saurara game da hajjin baɗi.

Daga nan ya shawarci maniyyatan da ke da ra’ayin karɓar kuɗinsu da su rubuta takarda zuwa ga Daraktan Hukumar na neman haka tare da sanya bayanan asusun ajiyarsu na banki da kuma shaidar risit.

Haka nab, ya ce ana iya aika takardar ta hannun jami’an hukumar na shiyyoyi da ke ƙananan hukumomi inda asali a nan aka yi biyan.

A ƙarshe, Aliyu ya ce maniyyatan da ba su asusun ajiya a banki ana buƙatar su rubuta takarda zuwa ga hukumar suna masu ba ta izinin mai da musu kuɗaɗen ta wani asusu na daban tare kuma da ba da cikakken bayanin asusun da za su yi amfani da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here