YANZU-YANZU: Saudi Arebiya ta janye wasu dokokin korona da ta sanya a masallatai

0
117

Gwamnatin Saudi Arebiya ta bada umarnin janye wasu dokoki na cutar korona da ta sanya a masallatai a faɗin ƙasar, Hukumar Kula da Harkokin Addinai ta ƙasar ce ta bayyana hakan ranar Lahadi.
Haka-zalika sashin wa’azi da faɗakarwa na Hukumar kula da Addinin Musulunci ta buɗe masallatai da dama bayan da ta bada umarnin rufe su na wucingadi domin a yi musu feshin magani.
Waɗannan sune dokokin da Saudiya ɗin ta janye kuma janyewar ta nan-take ce:

1- Dawo da guraren ajiye Al-Ƙur’ani

2- An cire taƙaita lokaci tsakanin kiran sallah da iƙama da kuma huɗubar sallar Juma’a.

3- An dawo da yin wa’azi a masallatai.

4- An cire sharaɗin nan na soke sahun sallah ɗaya tsakanin sahohin sallah.

5- An dawo da ajiye ruwa da firjina a masallatai.

6- Za a riƙa buɗe masallatai sa’a ɗaya kafin sallar Juma’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here