Soke Hajjin Bana: Gwamnan Jigawa, Badaru ya bada umarnin dawowa da maniyyata kuɗaɗen su

0
364

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru ya baiwa Hukumar Jin Daɗi da Walwalar Alhazai ta jihar da ta maidowa da maniyyatan da suka biya kuɗaɗen zuwa aikin Hajjin 2020 da 2021.

Shugaban Hukumar, Alhaji Sani Alhassan Muhammad, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Dutse.

Ya bayyana cewa gwamnan ne ya bada sahalewar biyan maniyyatan kuɗaɗen su.

Ya yi bayanin cewa duk maniyyatan da suke son karɓar kuɗaɗen su da suka biya na Hajjin 2020 da 2021 su tuntuɓi ofisoshin shiyya-shiyya ko Shalkwatar hukumar da ke birnin Dutse.

Ya kuma ƙara da cewa duk waɗanda suke son su ci gaba da ajiyar kuɗaɗen a hannun hukumar har zuwa hajjin baɗi, to suma suna da damar yin hakan.

Shugaban hukumar ya yi kira ga maniyyatan da suka yi allurar rigakafin Korona karo na farko da su je a cikashe musu karo na biyu domin amfanin ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here