Gwamnan Katsina ya bada umarnin dawowa da maniyyatan Hajjin 2020/2021 kuɗaɗen su

0
357

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bada umarnin a fara biyan maniyyatan jihar da suka biya kuɗin aikin Hajji na shekarun 2020 da 2021 haƙƙunan su.

Shugaban Hukumar Hajji ta Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ne ya shaidawa manema labarai a ranar Talata.

Ya ce duk maniyyacin da ya ke da niyyar karɓar kuɗin nasa to ya aika takardun neman biyan zuwa ofishin shiyyar da ya ke.

Kusan maniyyata 2,600, waɗanda suka ajiye kuɗin nasu tun daga shekarar 2020 zuwa 2021 ne za a biya su haƙƙunan su.

Kuki ya ƙara da cewa gwamnan ya bada umarnin kulawa da waɗanda za su cigaba da ajiye kuɗin nasu har zuwa Hajjin 2022, inda ya bada umarnin a basu kyakkyawar kulawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here