Saudi Arebiya ta bayyana cewa ta damƙe mutane 52 sakamakon karya dokokin ta na Hajjin 2021.
Wadanda aka kama ɗin sun shiga komar ma’aikata ne sakamakon shiga gurare masu tsarki ba tare da shaidar izini ba.
Hakan ya saba da dokokin Hajjin bana da ƙasar ta gindaya.