HAJJIN BANA: Jami’in lafiya ɗaya ne zai riƙa kula da kowacce tawogar alhazai 20

0
342

Saudi Arebiya ta bayyana cewa za ta sanya jami’in lafiya guda ɗaya ya kula da kowacce tawoga ta alhazai ashirin (20).

Ƙasar ta bayyana hakan ne a shafin ta na yanar gizo a wani mataki na tsaurara matakan kariya ga kamuwa da annobar korona.

“Za a sanya jami’i ga kowacce tawoga ta alhazai 20, wanda zai zama shine mai kula da lafiyar su wanda zai riƙa nuna musu yadda za su yi amfani da sabbin tsare-tsaren da aka yi.

“Haka kuma jami’in zai riƙa nusar da alhazan yadda za su riƙa ɗaukar matakan kariya yayin zuwa guraren ibada a yayin aikin Hajjin” in ji Hesham Saeed, kakakin Ma’aikatar Hajji da Ummara.

Ya kuma bayyanawa gidan telebijin na Al Ekhbariya cewa an samar da hanyoyin yin ɗawafi guda 25 a harabar masallacin Harami da ke Makkah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here