HAJJIN BANA: Alhazai za su fara ziyara zuwa Harami daga ranakun 17 da 18 ga Yuli

0
206

Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta bayyana cewa a ranakun 17 da 18 na watan Yuli ne za a fara tarbar alhazai a cibiyoyi huɗu, kafin daga bisani a ɗauke su zuwa Masallacin Harami na Makkah domin yin ɗawafi kana a kai su gurare masu tsarki na ziyara.

An baiwa ƴan ƙasashe 150 shaidun izini domin yin aikin Hajjin inda aka fi maida hankali a kan waɗanda basu taɓa yin aikin Hajji ba da kuma sauran rukunnai na masu shekaru.

Ma’aikatar kuma ta yi kira ga waɗanda aka baiwa sahidun izinin yin aikin Hajji da su je cibiyoyin yin rigakafin Korona mafi kusa domin su a yi musu allurar a karo na biyu sannan su yi biyayya ga sharuɗɗan kariya daga cutar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here