HAJJIN BANA: Sarkin Makka ya danƙa Kiswa ga babban maigadin Ka’aba

0
1414

Sarkin Makka, Yarima Khalid Al-Faisal, wanda shine mai baiwa Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu shawara, ya danƙa Kiswa (mayafin lulluɓe Ka’aba) ga Saleh Al-Shaibi, babban maigadin Ka’aba ranar Lahadi.

Al-faisal ya danƙa mayafin ne a madadin Sarki Salman, Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu a wani taro da a ka yi a ofishin sa na masarauta da ke Jidda.

Shugaban Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu, Sheikh Dr. Abdulrahman Al-Sudais ya ce miƙa mayafin wata manuniya ce cewa masarautar Saudi Arebiya na baiwa Ka’aba cikakkiyar kulawa.

Ya kuma nuna ƙwazon masarautar ta hanyar samun cikakkiyar dama ta ganin ana ɗinka mayafin Ka’aba ɗin mai tsarki a ginin Sarki Abdulaziz .

Kiswa, mayafin da a ke ganin na ɗaya daga cikin ayyukan zane a tarihin musulunci, na da tsayi na mita 14 daidai da tsayin Ka’aba, sannan faɗin sa ƙafa 47 ne yadda zai isa a rufe gaba ɗaya kusurwa huɗu na Ka’aba.

Rabin mayafin daga sama mai faɗin ƙafa 95, an yi masa ado mai ɗauke da ayoyin ƙur’ani da aka rubuta su da zare mai ruwan gwal, kuma nauyin mayafin ya kai kilogram 120.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here