HAJJIN BANA: Ayarin farko na alhazai ya kammala ɗawafin sauka

0
366

…yayin da rukunin farko na alhazai 36,000 ya isa Minna

Ayarin farko na alhazan Hajjin bana sun kammala ɗawafin sauka harami, wanda da larabci ake kira Tawaf Al-ƙudum.

Rahotanni sun bayyana cewa alhazan sun yi ɗawafin cikin sauƙi da kwanciyar hankali a wani yanayi na ƙarfafa ayyuka da tsare-tsaren kariya daga cutar korona.

Kakakin Babban Ofishin Shugabancin Masallatan Harami Guda Biyu, Hani Haidar ya bayyana cewa an samar da layika a cikin haramin wanda zai sauƙaƙawa alhazai yin ɗawafi.

Ma’aikata 60 aka ware domin kula da masu yin ɗawafin don ganin an samar da tazara tsakaninsu.

Da ya ke nuna cikakken goyon baya daga Masarautar Saudi Arebiya, Kakakin ya jaddada ƙudurin ofishin na samar da gangariyar hidima ga alhazai da kuma samar musu da muhallin yin ibada da ya dace kuma cikin ƙoshin lafiya.

A nashi ɓangaren, Daraktan Kula da Cunkoso na Babban Masallaci Mai tsarki, Osama bin Mansour Al-Hujaili ya bayyana sama da ma’aikata 500 aka ɗauka suke jigilar alhazai tun a farkon watan nan a cibiyoyi uku.

Ya ƙara da cewa an tanadi ƙofar Al-Marwah domin fita daga harami bayan an kammala ɗawafi a wani mataki na tabbatar da kula da bada tazara tsakanin alhazai.

A wani ɓangaren kuma, kimanin alhazai 36,000 ne suka sauka a mina inda za su kwana a nan , zuwa gobe kuma sai su fita filin Arfa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here