Bayan sun yi jifa na farko, alhazai sun dawo rumfunan su domin ci gaba da zaman Mina, wanda aka fi sani da tashreeq, wato kwanaki 3 bayan an yi idin babbar Sallah.
An rawaito cewa zaman na kwanaki 3 ko 2, ana yin shi ne cikin ɗaukar matakan kariya daga cutar korona.
An kuma hango alhazan cikin farinciki da kwanciyar hankali suna ta ɗaukar hotunan gine-ginen jamrat da kuma rumfunan su.
Sannan na’urar yayyafin ruwa na ci gaba da sanyaya jikin alhazai bayan da yanayin zafi ya kai kimanin maki 38.
An rawaito cewa alhazan sun bayyana jin daɗi da gamsuwa da yadda ake tafiyar da aikin Hajjin, inda yawancin su suka nuna cewa babu wata matsala da suka fuskanta.