HAJJIN BANA: Ma’aikata mata 825 ne suke yi wa alhazai hidima a babban masallacin Harami

0
249

Kimanin mata 825 ne mahukunta a Saudi Arebiya su ka ɗauka aiki domin yiwa alhazai mata hidima a Masallacin Harami da ke birnin Makka a wani mataki na bunƙasa hanyoyin yin aikin Hajji mai inganci, in ji wani ƙusa a Saudi Arebiya.

Daga cikin ma’aikatan awai mata 227 da aikin su shine tarbar alhazai mata tun daga bakin ƙofar shiga Harami, inda su ke bawa baƙin jaka da za su ajiye kayayyakin su gami da bin matakan kariya daga cutar korona, in ji Wadha bint Abdul Rahman, shugabar ɓangaren mata ma’aikata.

Haka kuma wasu matan su 500 aikin su shine goge-gogen ƙasa da sinadarin kashe kwayoyin cuta sannan su riƙa share shimfiɗun ɓangaren mata na masallaci mai tsarki, wannan ya haɗa da jami’an tsaro mata su 48, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiya SPA ya rawaito ta bakin ta.

A yau ne Alhazai mazauna Saudiya da ke aikin Hajjin bana suke dawowa Haramin domin yin ɗawafi bayan sun yi kiran shaiɗan a Minna, kimanin kilomita 7 daga Makka, inda wannan wani rukuni ne na aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here