Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu, Sarki Salman na Ƙasar Saudi Arebiya ya yi jawabi ranar Talata inda ya taya ƴan ƙasa, baƙi mazauna ƙasar, alhazai da kuma ɗaukacin al’ummar duniya murnar Babbar Sallah.
A jawabin nasa, Sarki Salman ya yi addu’ar zaman lafiya, rahma da albarka ga dukkan kowa da kowa.
Ya kuma yiwa alhazan da ke aikin Hajjin bana addu’a da kuma ma’aikatan da suke musu hidima.
Ya kuma godewa Allah a bisa namijin ƙoƙarin da ƙasar ta yi wajen samun nasarar rage illar annobar korona a ƙasar.
Sarki Salman ya kuma bayyana cewa kasar na ƙoƙarin bunƙasa garkuwar jikin ƴan ƙasar domin kariya daga kamuwa da korona3, inda ya bayyana cewa kasar za ta samar da allauran rigakafin Korona har miliyan 22 domin yiwa al’umma.
A ƙarshe ya yabawa ƙasashen duniya wajen goyon bayan tsare-tsaren Saudiya na yin aikin Hajji a cikin annobar korona.