Masu iya magana na cewa “komai ya yi farko, zai yi ƙarshe”
Haka ne ya faru a Hajjin 2021 (Hajjin bana) yayin da ibadar ta zo ƙarshe bayan da tuni alhazai su ka fara barin Mina tun a yammacin Alhamis, lamarin da ke nuni da cewa an fara kammala kwanakin tashreeq.
Bayan da alhazan suka kammala jifa na ƙarshe, za su zarce zuwa harami domin yin ɗawafin bankwana, inda hakan ke nuni da kammala aikin Hajjin bana, wanda aka rage yawan alhazan zuwa dubu sittin sakamakon annobar korona.
An ga alhazan na cike da shauƙi da kuma farincikin kammala wannan ibadar da ba kowa ke samun damar yin ta ba.
Alhazan sun isa Harami ne a rukuni-rukuni, inda Babban Ofishin Shugabancin Masallatan Harami Guda Biyu ya tanadi ingantaccen tsari domin alhazan a babban masallacin.
Tun a farko Osama Al-Hujaili, Darekta na Sashin Kula da Cunkoso ya bayyana cewa rukunin farko na akhazan da za asu yi ɗawafin bankwanan za su taru ne a guraren taruwa guda uku da aka tanada a Shobaika, Kudai da Ajyad da suke jikin masallacin Harami.
A ƙarshe dai, tun a ranar Alhamis wasu akhazan su ka fara barin Makka, inda waɗan da su ke daga gurare masu nisa daga garin za su jira har sai yadda aka tsara jadawalin tashin su a jirgin sama.