Ba sai alhazai sun sake gwajin korona da killacewa ba bayan Hajji- Ministan Lafiya

0
290

Alhazan da ke dawowa gida bayan kammala aikin Hajjin bana ba sa buƙatar su sake yin gwajin cutar korona ko kuma su killace kan su, in ji Mataimakin Ministan Lafiya da Kariyar Al’umma na Saudi Arebiya, Dr. Abdullah Asiri.

“Da yawan alhazai na tambayar ko da buƙatar su sake yin gwajin korona da killacewa bayan sun koma ga iyalansu.

“Tunda dai an yi musu allurar rigakafin korona, to babu wata buƙata ta a sake musu gwaji sai dai idan sun nuna wata alama ta korona ɗin a makonni biyu bayan dawowar su.

A wani fannin kuma, kusan kashi 92 ne na waɗan da su ka ce za ai musu rigakafin kuma aka yi musu ɗin.

Asiri ya ce “Dalilai uku muhimmai da suka ja hankalin waɗanda a da suka ƙi yin allurar daga baya kuma suka je akai musu sune.

“Yarda da kuma ƙarin gwiwa daga iyalan su waɗan da aka yi musu rigakafin. Na biyu kuma kishin ƙasa da al’umma na ƙarshe kuma shine ɓangaren tattalin arziki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here