#Umrah2021
Kwanaki kaɗan bayan kammala aikin Hajjin 2021, kamfanonin jigilar Ummara sun shirya tsaf domin tarbar alhazan Ummara da suka samu cikakken rigakafin korona daga 9 ga watan Agusta.
Alhazan dai za su samu damar samun harkoki har wajen 500 ta hanyar amfani da manhajar yanar gizo-gizo, inda ta nan ne za su yanki tikitin jirgin sama, harkokin sufuri, otal da kuma ganawa da kamfanonin jigilar Ummara.
Hani Al-Omairi, wani ƙusa a Babban Kwamitin Ƙasa na Hajji da Ummara da kwamitin kula da harkokin otal a Makka ya shaidawa jaridar Alarabiya cewa za a samar da kusan shafukan yanar gizo-gizo da manhajoji talatin domin kama ɗakunan a otal da kuma sufuri.
“An fara bawa ma’aikata da dama horo a kan lafiya da kuma kula da cinkoso yayin da kamfanoni ke nasu shirin. Ma’aikatar harkokin Hajji da Ummara ta yi shiri mai inganci domin tuni an kammala tsare-tsaren da za a baiwa kamfanonin da masu ruwa da tsaki.”
A nashi ɓangaren, Muhsin Tulta, Shugaban Gidauniyar Kulawar Hajji da Ummara ta Duniya ya bayyana cewa dawowar alhazan ƴan ƙasashen waje zai kasance ne a ƙarƙashin bada horo kan kariya daga kamuwa da korona.
Ya ƙara da cewa ƙirƙiro da fasahar sa ido a ɗaukacin lokutan Ummara ɗin da sauran matakai zai taimaka wajen sauƙaƙa aikin.