Ƴancin Samun Bayanai: Hajj Reporters na neman bayanai kan kuɗaɗen da maniyyata suka biya

0
460

…ta rubutawa hukumomin Hajji na jihohi

Independent Hajj Reporters, ƙungiya mai zaman kan ta da ke sa ido da kawo rahotanni a kan harkokin Hajji da Ummara a Nijeriya ta rubutawa wasu Hukumomin Jin Daɗi da Walwalar Alhazai a kan dawo da kuɗaɗen da maniyyata su ka bayar na zuwa aikin Hajji 2020 da 2021 da aka soke.

Yayin da ta dogara da ƙarfin dokar Ƴancin Samun Bayanai ( FOI), Hajj Reporters ta aikewa hukumomin Jin Daɗin Alhazai na jihohin da abin ya shafa da su da su ba ta bayanai a kan yadda dawowa da maniyyata kuɗaɗen su ke gudana.

A wasiƙar da Shugaban ƙungiyar na ƙasa ya sa hannu, ta dogara ne da sashi na ɗaya da na biyu na dokar Ƴancin Samun Bayanai (FOI), 2011.

“Duba da sashi na ɗaya da na biyu na dokar Ƴancin Samun Bayanai (FOI) 2011, mun rubuta muku wannan wasiƙa domin neman bayanai a kan kuɗaɗen Hajji da maniyyata suka biya na Hajjin 2020 da 2021 wanda aka soke su sakamakon annobar korona.

“Muna so mu san adadin maniyyatan da suka yi rijista da Hajjin 2020 da 2021 da kuma kuɗin da kowanne maniyyaci ya biya. Muna so kuma mu san maniyyata nawa ne su ka ci gaba da ajiye kuɗaɗen su zuwa Hajjin 2021” in ji wani ɓangare na wasiƙar.

Hajj Reporters kuma ta nemi hukumomin da su bata bayani a kan adadin maniyyatan da suka yi rijistar Hajjin 2021 da kuma kuɗin da kowanne maniyyaci ya biya.

Sannan kuma ta nemi bahasi a kan adadin maniyyatan da su ka yi rijista da tsarin Adashin Gata na Hajji (Hajj Savings Scheme) da kuma adadin kuɗin da kowanne maniyyaci ya biya.

Sannan kuma ƙungiyar ta nemi hukumomin da su bata bayani a kan kuɗin ruwa, idan a kwai, da kuɗaɗen maniyyatan suka tara a bankuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here