Shugaban kula da Harkokin kula da Masallatan Harami Guda Biyu, Sheikh Dr Abdul Rahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya faɗawa ɗaukacin hukumomin da ke kula da harkar Ummara da su yi shirin ƙarshe don tarbar alhazan Ummara daga wajen ƙasar, wacce za a fara daga ranar ɗaya ga watan Muharram.
Sheikh Sudais ya ƙara da kira ga hukumomin da su yi kyakkyawan shiri tare da samar da tsare-tsaren aiki da za su taimaka musu wajen tallafawa alhazan gudanar da ayyukan ibadunsu ba tare da samun wani cikas ba.
Sheikh Sudais ya jaddada cewa wannan falala ce babba da Allah Ya ƙaddari baƙi daga waje su samu zarafin zuwa umurah a ƙasa mai tsarki.
Ya ce ana fatan komai ya koma daidai kamar yadda yake a can baya kafin ɓullar annobar korona wadda ta yi sanadiyyar rage adadin maniyyata daga waje zuwa ƙasa mai tsarki.
Don haka, ya yi kira ga dukkan hukumomin da lamarin ya shafa da su ƙara himma wajen shirye-shiryen karɓar maniyyatan na Umura tare da la’akari da dokokin yaƙi da yaɗuwar cutar korona da aka gindaya.
A ƙarshe, Sudais ya yi addu’ar Allah Ya yaye wa al’ummar Musulmi damuwarsu, kana ya albarkaci ƙoƙarin shugabanni masu jagorancin harkokin ƙasa mai tsarki.