Bayan watanni 18, daga gobe Saudiya za ta fara karɓar neman izinin yin Ummara daga ƙasashen waje

0
424

Saudi Arebiya za ta fara karɓar neman izinin yin Ummara daga gobe Litinin, inda za ta fara da adadin alhazai dubu sittin (60,000), kuma za ta kasa ranar yin aikin zuwa lokuta 8, inda zai kai adadin alhazai miliyan biyu a wata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudi a jiya Asabar ya rawaito cewa Saudi za ta fara karɓar neman izinin yin Ummara daki-daki daga gobe Litinin, 9 ga watan Agusta “inda za ta fara da adadin alhazai dubu sittin, kuma za ta kasa ranar yin aikin zuwa lokuta 8, inda zai kai adadin alhazai miliyan biyu a wata.”

Kusan shekara ɗaya da rabi kenan da hukumomi a Saudiyya suka dakatar da zuwan alhazai ƴan ƙasashen waje sakamakon annobar korona da ta mamaye duniya.

Sai kuma a bara ƙasar ta sake buɗe yin Ummara ɗin amma ga mazauna cikin ƙasar bayan da ta dakatar da yi kwata-kwata.

Mataimakin Ministan Hajji da Ummara, Abdul-Fattah bin Suleiman Mashat, ya bayyana cewa waɗanda za su nemi iznin yin Ummara sai sun nuna takardar shaidar yin allurar rigakafin korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here