Saudi ta sanar da sabbin dokokin yin Ummara

0
262

…ta ƙara adadin alhazan Ummara zuwa miliyan biyu a wata

Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta sanar da sabbin dokokin yin Ummara, waɗan da za su fara aiki daga ranar Litinin, 1 ga watan Muharram, wanda ya zo daidai da 9 ga watan Agusta, 2021.

Sabbin dokokin sune kamar haka:

-Ƙara adadin alhazai mazauna ƙasar zuwa dubu sittin daga ranar Litinin.

-Ƙara adadin alhazai zuwa miliyan biyu a wata da zai fara aiki daga ranar Litinin.

-Babu iyaka ga adadin alhazan da za su yi Ummara a bana.

-Dole ne sai alhaji ya yi cikakken rigakafin korona.

-Aika neman gurbin yin Ummara, ziyara da sallah a Rawdha da Masallaci Mai Tsarki za a yi shi ne ta manhajar Eatmarna ko Tawakalana.

-Ba za a bar yara ƴan ƙasa da shekara 17 su shiga Masallatan Harami ba.

– Daga Litinin za a fara tarbar alhazai daga ko ina a faɗin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here