Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta yi mi’ara koma baya a kan matakin hana yara ƴan ƙasa da shekara 18 su yi Ummara a bana.
Amma kwatsam sai a ka ji ma’aikatar ta canja matsaya, inda ta ce yara ƴan sama da shekara 12 ƴan ƙasa da kuma baƙi amma mazauna Saudiya za su yi Ummara, ziyara da kuma yin salloli a Rawdah da kuma Masallatan Harami Guda Biyu.
Sai dai kuma Ma’aikatar ta ce ba za a bar yaran ƴan sama da shekara 12 ɗin ba har sai an yi musu allurar rigakafin korona a ƙalla sau ɗaya.