DAWOWAR UMMARA: Kamfanin sufuri na Firdausi ne ya fara buga biza ga alhazan Nijeriya

0
257

Kamfanin sufuri na Firdausi, wanda a ka fi sani da Firdausi Transport Service Ltd. ya kasance shine na farko da ya samarwa alhazan Ummara na Nijeriya biza bayan da Saudi Arebiya ta ɗage dakatarwar da ta yi daga yin Ummara, sannan ta ƙara yawan alhazan Ummara ɗin zuwa miliyan biyu a wata.

Wani samfurin bizar da Shugaban kamfanin, Alhaji Aliyu Jega ya aikewa da Hajj Reporters ya nuna cewa an bugawa wani alhaji mai suna Ibrahim Abdullahi, mai ɗauke da lambar biza 6074168226.

Samfurin ya nuna cewa bizar ta kwanaki talatin ce da za ta fara daga 9 ga watan Agusta zuwa 8 ga watan Satumba, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here