Yadda mu ka yi jigilar alhazan farko na Ummara daga Nijeriya- Kamfanin Oasis

0
239

Shugaban kamfanin Oasis air services, Alh Abubakar Ahmed, ya ce sun sha aiki ba dare, ba rana tun bayan da Saudiyya ta ba da sanarwar ɗage dokar hana zuwa Umura ga maniyyatan ƙasashen waje.

Abubakar Ahmed ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da ya yi da HAJJ REPORTERS a safiyar Asabar.

Ya ce, “Muna matuƙar farin cikin samun zarafin jigilar tawagar farko na alhazan Umura na shekarar 1443 AH, inda muke fatan ƙarshen annobar korona ya zo kenan.”

HAJJ REPORTERS ta ruwaito cewa tawagar farko ta maniyyatan Umura daga Nijeriya ta isa Ƙasar Saudiyya a wannan Asabar, inda ‘yan tawagar suka damu kyakkyawar tarba daga jami’an Saudiyya a babban filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah.

Abubakar Said ya ce “Adadin maniyyata Umura su biyar da kamfanin Oasis Air Services ya tsara tafiyarsu, kamfanin Qatar Airline ya yi jigilarsu daga Babban Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here