Rukunin farko na alhazan ummara ya sauka a Madina

0
325

Rukunin farko na mahajjatan Umurah daga ƙasar Iraƙi ya isa Babban Filin Jirgin Sama na Yarima Mohammad Bin Abdulaziz da ke birnin Madinah a Juma’ar da ta gabata don gabatar da Umura da kuma gaisuwa ga Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa tsarkaka.

Rukunin ya ƙunshi mahajjata 100 daga Irbil, a tarayyar Iraƙi.

Jami’ai ne suka tarbi mahajjatan tare da kiyaye matakan kariya daga kamuwa da cutar korona da aka shimfiɗa.

Sashen ba da fasfo na filin jirgin sama na yin dukkan mai yiwuwa don bai wa mahajjatan dukkan kulawar da ra dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here