Sama da wata 1 hukumomin Hajji na jihohi sun gaza bada bayanai kan dawo da kuɗaɗen maniyyata

0
604

Hajj Reporters, Ƙungiya mai zaman kanta da ke kawo rahotanni a kan Hajji da Ummara a ciki da wajen Nijeriya ta aika wasiƙar tunatarwa ga rukunin farko na Hukumomin Kula da Walwalar Maniyyata na Jihohi dangane da neman cikakken bayani kan batun maida wa maniyyata kuɗaɗensu na Hajjin 2020/2021.

Tun farko, ƙungiyar ta rubuta wa hukumomin da lamarin ya shafa takardar na neman a bahasi a kan maida kuɗaɗen hajji ga maniyyata bayan Saudi Arebiya ta soke yin aikin Hajji gabƴan ƙasashen waje amma haƙar ta ba ta cimma ruwa ba.

Wannan bayani na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kodinetan Independent Hajj Reporters (IHR) na ƙasa, Ibrahim Muhammad ya fitar a ranar Litinin.

Waiƙar mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Augustan 2021 ta nuna cewa, “Dangane da wasiƙarmu mai ɗauke da kwanan wata 30 ga Yunin 2021, kuma la’akari da sashe na 1 da na 2 na Dokar ‘Yancin Faɗar Albarkacin Baki (FOIA) ta 2011, mun yi wannan wasiƙar ce don tunatar da ku game da bayanan da muka nema kan sha’anin maniyyata Hajjin 2020 da 2021, wanda aka hana ‘yan ƙasashen ƙetare zuwa saboda annobar korona.

Bayanan sun hada da: “Adadin maniyyatan da aka yi wa rajista dangane da Hajjin 2020 da na 2021 a jihohinku;

“Adadin maniyyatan da aka samu maida musu kuɗaɗensu dangane da Hajjin 2020, da kuma adadin maniyyatan da suka ci gaba da ajiyar kuɗinsu don Hajjin 2021;

“Adadin maniyyatan da suka suka yi rajista a Hajjin 2021 da kuma adadin kuɗin da kowannensu ya soma biya;

“Adadin maniyyatan da suka shiga shirin adashin gata na Hajj Saving Scheme a jihohinku da kuma abin da kowannensu ya biya.

“Adadin maniyyatan da suka biya rabin kuɗaɗensu ta hannun NAHCON ya zuwa watan Yunin 2020;

“Jerin sunayen bankunan da hukumar alhazai ta jiha ta kai kuɗaɗen da maniyyatan suka biya ajiya gami da ruwan da ya hau kuɗin idan akawai.

Sanarwar manema labarai da IHR ta fitar a ranar Litinin ta nuna cewa tun farko an tura wa wasu jihohi takardar neman bayanai da suka haɗa da jihar Kaduna, Adamawa, Niger, Kogi, Bauchi, Kwara, Sokoto, Kebbi, Borno, Zamfara, Lagos da kuma jihar Taraba.

Idan dai za a iya tunawa, tun a ranar 24 ga Mayun 2011 ne Majalisar Tarayya ta amince da dokar FOI wadda tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya rattaba wa hannu a ran 28 ga Mayu, 2011.

Babban ƙudurin wannan doka shi ne bai wa hadiman jama’a damar shiga da fita don samo bayanan da jama’a ke da buƙatar sani.

An kafa dokar FOI don daƙile yadda masu riƙe da ayyukan gwamnati kan aikata yadda suka ga dama da haƙƙoƙin gwamnatin da suka rataya a kansu.

Kuma domin cin moriyar wannan doka ta FOI, sharaɗi ne a tura da wasiƙa ta hanyar da ta dace zuwa inda ake da buƙata tare da bayyana irin bayanan da ake nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here