Labarin cin dukan Sudais ƙarya ne, farfagandar maƙiya addinin Musulunci ce- Sheikh Muhammad

0
101

Fitaccen malamin addinin Islama a Kano, Sheikh Abdulmudallib Muhammad, ya ƙaryata fefen bidiyon da aka yi ta yaɗawa mai nuni da wai an lakaɗa wa Sheikh Abdurrahman Al- Sudais duka a gaban iyalinsa.

Hajj Reporters ta rawaito yadda aka yaɗa wannan bidiyon a kafofin sadarwa mai nuni da lokacin da wai Shugaban Kula da Masallatan Harami Guda Biyu, Sheikh Abdurrahman Al-Sudais, ke cin bugu a hannun jami’an tsaron Saudiyya.

An yaɗa bidiyon ne ɗauke da wani saƙo da ke cewa wai an daki Al-Sudais a bisa umarnin Yarima Muhammad Bin Salman saboda ya faɗi abin da ya saɓa wa Masarautar Saudiyya, inda wai ya nuna ɓacin ransa a kan matakin da ƙasar ta ɗauka na rage adadin mahajjatan 2021 zuwa mutum 60,000.

Amma, Sheikh Muhammad ya fito ya ƙaryata wannan bidiyon mai tsawon sama da minti 4, yana mai cewa bidiyon na ƙarya ne kuma sharri ne kawai da maƙiya addinin Musulunci ke kitsawa suka kuma yaɗa don cimma mummunan manufarsu.

A cewar Malamin, tun daga ranar 11 ga Yunin da ya gabata wanda ya yi daidai da 1 ga watan Zul-q’ada, 1442 AH, wato kimanin kwanaki arba’in kenan gabanin Hajjin bana, Sheikh Sudais bai jagoranci Sallar Juma’a ba balle kuma ya gabatar da huɗuba.

Sheikh Muhammad, wanda ke fassara huɗubar da akan gabatar a Masallacin Ka’aba duk Juma’a a gidan rediyon Rahma 97.3 FM da ke Kano, ya ce Sheikh Sudais ya kasance mai yabawa Gwamnatin Saudiyya bisa irin ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da yaɗuwar cutar korona a ƙasar.

A cewarsa, “Duk ƙarya ne. Bidiyon da ake yaɗawa na ƙarya ne, sharrin ‘yan Shi’a ne kawai. Lokaci na ƙarshe da Sudais ya jagoranci Sallar Juma’a da kuma gabatar da huɗuba, shi ne ranar 11 ga Yunin 2021, wanda ya yi daidai da 1 ga Zul-q’ada, 1442 AH, kimanin kwanaki 40 gabanin Hajjin bana.

“Haka nan, yayin huɗubarsa a wancan lokaci har da yabo ya yi wa Gwamnatin Saudiyya bisa ƙoƙarinta wajen tsabtace muhalli inda ƙasar ta ke feshin maganin kashe ƙwayoyin cuta tare da feshe ko’ina, duk da zummar yaƙi da yaɗuwar cutar korona.

“Tsarki ya tabbata ga Allah, kimanin shekaru 10 kenan ina bibiyar duka huɗubar da ake gabatarwa a Masallacin Harami duk Juma’a, amma ban taɓa jin inda Sheikh Alsudais ya soki Gwamnatin Saudiyya ba kan batun rage yawan mahajjata.

“Wannan ala’mari ya ɗauki hankalin jama’a sosai har ya kai ga ana ta turo mini tambayoyi ta WhatsApp da Facebook don sanin gaskiyar magana. Wannan ne ya sa na fito don in ƙaryata labarin don wayar da kan jama’a.”

Baya ga ƙaryata bidiyon, Sheikh Muhammad ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su yi hattara da ire-iren waɗannan labarin na ƙarya waɗanda akan yaɗa su don cin mutuncin Musulunci.

Haka nan, ya ce har yanzu tushen asalin labarin ba a bayyane yake ba wanda a cewarsa, wannan kaɗai ya ishi duk mai tunani sanin cewa labarin na bogi ne tun da a bayyana tushensa ba.

Ya ci gaba da cewa, “Na musamman aka yaɗa wannan labarin ƙarya a kafafen sadarwa domin ɓatar da Musulmi wanda wasu ɓatagari suka yi don shafa wa Musulunci baƙin fenti da kuma ɓata mutuncin Gwamnantin Saudiyya.

“Don haka ina kira ga ‘yan’uwana Musulmi, maza da mata kan cewa kowa ya nastu ya kwantar da hankalinsa saboda wannan batu ƙarya ne, ba gaskiya ba ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here