A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne a ka dawo da majalisun da a ke yi na haddar Alqur’ani mai girma, bayan an dakatar da yin karatun kusan shekaru biyu da su ka gabata a wani mataki na yaƙi da annobar korona.
Wani ƙasa a babban ofishin da ke kula da harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya bayyana cewa an sake buɗe majalisun in da mutane za su riƙa ɗaukar darussan Alqur’ani daga ƙarfe 4 zuwa karfe 8 na yamma.
“Sashin ya ɓullo da wasu sabbin dabaru domin dawo da majalisun karatun Alqur’ani a mataki-mataki a babban masallacin,” in ji Badr Al Muhammadi, wan da shi ne shugabanin sashin.
Ya ce mataki na farko shine mutum takwas ne kacal za su riƙa ɗaukar darussan karatun kuma sau ɗaya tak a rana, in da ya ƙara da cewa hakan wani mataki ne na kare lafiyar al’umma.
A na shi ɓangaren, gidan telebijin na Saudiya, Al Ekhbariyya ya bayyana cewa sai waɗanda a ka yiwa cikakkiyar allurar rigakafin korona ne za su riƙa ɗaukar darussan Alqur’ani a masallacin.
A watan da ya gabata ne Saudiya ta dawo da halartar wa’azuzzuka a masallacin mai alfarma bayan an samu tsaiko na kusan shekaru biyu.