Korona: Ma su harkokin Hajji sun fara shirin amfani da sabbin tsare-tsare

0
243

Bayan canje-canjen da annobar korona ta kawo da kuma yadda ta hana cakuɗuwar al’umma domin daƙile yaɗuwarta, ma su harkokin Hajji sun bayyana cewa su na shirye-shiryen bin sabbin tsare-tsaren.

Ƙungiyar Ma su Harkokin Hajji da Ummara a Nijeriya (AHOUN), reshen Kudu maso Yamma ne su ka bayyana hakan a wani taron ma su ruwa da tsaki da a ka yi a masallacin Ansar-Ud-Deen da ke Surulere, Jihar Legas, in da su ka bayyana tsare-tsaren yadda za su ilmantar da ma su harkokin Hajji da Ummara domin shirye-shiryen da ake yi saboda korona.

Wa ta sanarwa da aka fitar ta rawaito ta bakin Mataimakiyar Shugaban Ƙungiyar ta Ƙasa, Alhaja Mariam Popoola na cewa an haɗa taron ne a kan buƙatar aiwatar da sabbin tsare-tsaren da aka ɓullo da su sakamakon annobar korona wacce ta sanya dukka ƴan ƙungiyar zaman kashe wando ma tsawon shekaru biyu.

“Mu na don dukkan masu harkokin Hajji da Ummara da su ke da lasisi su zo a tattauna matsalolin da suke fuskantar mu gaba ɗaya. Tsawon shekaru biyu da suka gabata, tabbasa annobar korona ta kawo mana naƙasu. Ta hana mu zuwa aikin Hajji. Wasu ma da iya harkar nan kawai su ka sani haka su ka zauna ba sa komai.

“Korona ta zo da sabbin ƙa’idoji, sabo da haka akwai abubuwa da yawa da sai ta kafar yanar gizo za yi su kuma ana ta ƙirƙiro da manhajoji. A wani mataki na tallafawa masu ƙaramin ƙarfi su je aikin Hajji, shine a ka ƙirƙiro da shirin Adashin Gata na Hajji”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here