Rawdah Travels za ta yi jigilar alhazan Ummara na Nijer

0
220

Kamfanin Harkokin Hajji da Ummara da ke Jihar Kano, Rawdah Travels and Tours Ltd. ya bayyana cewa a shirye ya ke ya fara jigilar alhazan Ummara na Jamhuriyar Nijer zuwa Saudi Arebiya.

Shugaban kamfanin, Alh Umar Abdulhadi ya shaidawa HAJJ REPORTERS cewa alhazan su biyar za su tashi ne ta jirgin Royal Air zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 10 ga watan Satumba.

Abdulhadi ya ce ” mun kammala duk wasu shirye-shiryen tafiya kamar su biza, tikiti da kuma tanadar masauki da motocin hawa a can ƙasa mai tsarki.

Hajj Reporters ta ga kofin bizar da aka bugawa wata mai suna RABI SALIFOU mai ɗauke da lamba 6074419267, wacce a ka buga a ranar 5 ga Satumba kuma za ta ƙare a ranar 5 ga Oktoba 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here