Saudi ta ƙara yawan alhazan Ummara zuwa 70,000 a rana

0
478

Ma’aikatar Harkokin Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta tabbatar da ƙara yawan alhazan Ummara zuwa dubu ɗari bakwai (700,000) a rana.

Ma’aikatar da ƙara da cewa za a bar wannan adadin, wanda ya ƙunshi ƴan ƙasa da baƙi, su yi aikin Ummara a rana, amma sai da cikakkiyar biyayya ga sharuɗɗan kariya daga kamuwa da korona da kuma sauran cututtukan da mahukunta ke ƙoƙari a kai.

Ma’aikatar ta kuma yi bayanin cewa za a iya neman gurbin yin aikin Ummara da yin Sallah a masallacin Harami ta manhajar Tawakkalna bayan ta Eatmarna.

A na shi ɓangaren, Dr. Saad Al-Muhaimid mataimakin riƙon ƙwarya na sakataren Ofishin kula da Masallatan Harami Guda Biyu ya bayyana cewa ƙara adadin alhazan Ummara zuwa 700,000 ya nuna irin jajircewar jagorancin ofishin na ƙara faɗaɗa hidima a Masallatan haramin biyu ma su tsarki domin akhazai su samu su yi ibada cikin kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here