Mu na daf da ƙara yawan alhazan Ummara zuwa 70,000 a rana- Masallacin Harami

0
423

Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya bayyana cewa ya shirya ysaf domin faɗaɗa yawan alhazan Ummara a masallacin Harami zuwa dubu saba’in (70,000) a rana.

Ofishin ya bayyana hakan ne bayan da a kwanakin baya ya ƙara yawan alhazan Ummara ɗin zuwa dubu sittin (60,000) a rana.

HARAMAIN SHARIFAIN ya rawaito cewa Kakakin ofishin, Mai girma Hani bin Hosni Haidar, a wata sanarwa ya ce ” Mun kammala shirye-shiryen ƙara yawan alhazan Ummara zuwa 70,000 a rana, kuma a ƙarƙashin sa idon Babban Shugaban Ofishin, Sheikh Dr. Abdul Rahman bin Abdulaziz Al-Sudais.”

Sanarwar ta kara da cewa ofishin ya samar da matakan kariya daga kamuwa daga cutar korona da su ka haɗa da samar da kyamara mai amfani da sanyi da kuma sauran na’urorin zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here