Saudiya, Nijeriya sun daƙile yunƙurin Hezbollah na safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudi

0
422

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudi Arebiya, Kanal Talal Al-Shalhoub ya bayyana cewa yunƙurin na yaƙi ayyukan ma su safarar miyagun ƙwayoyi da jami’an tsaro ke yi ya sanya an daƙile wani yunƙuri da wani gungun masu safarar miyagun ƙwayoyi ya yi ka shigar da wasu muggan ƙwayoyi da a ke zargin na ƙungiyar ya’n ta’adda ta Lebanon, wato Hezbollah ne.

Ana zargin cewa Hezbollah ɗin ta yi yunƙurin shigar da wata ƙwaya mai suna amphetamine har guda 451,807.

Al-Shalhoub ya ce an ɓoye ƙwayar ne a cikin wasu injina da aka yi safarar su ta ruwa zuwa Nijeriya, daga bisani kuma a kai su wata ƙasar, sannan a shigar da su cikin Saudi Arebiya.

Ya ƙara da cewa an kama ƙwayoyin ne a wani sumame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro na Nijeriya.

Kakakin ya yabawa haɗin kan da jami’an tsaron Nigeriya su ka bayar wajen bankaɗo ƙwayoyin da suke bugarwa, in da ya jaddada ƙudurin ƙasar Saudiyya na ci gaba da farautar irin waɗannan ɓata-garin da kuma daƙile safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here