Bizar Ummara 6,000 a ka baiwa alhazan ƙasashen waje a Muharram- Saudiya

0
66

Mataimakin Ministan Harkokin Hajji da Umurah na Saudiyya, Injiniya Hisham Saeed, ya bayyana cewa bizar Ummara 6,000 ne aka baiwa alhazan ƙasashen waje a watan Muharram.

Jaridar Okaz/Saudi Gazette ta ruwaito ministan na cewa, maniyyata Umurah daga ƙetare sun soma zuwa ne daga ƙasashe daban-daban bisa tsari da kuma dokokin kariya da kamuwa da kuma yaɗa cutar nan ta korona.

Injiniya Hisham Saeed ya ce, “Ma’aikatar Hajji da Umurah ta samar da tsarin yin Umurah mai inganci wanda ya yi daidai da dokokin kare lafiya.”

A cewarsa, “Ma’aikatar ta ba da muhimmanci kan ganin kamfanonin Umurah na Saudiyya sun ba da kulawa mai armashi ga maniyyata, kama daga masauki zuwa abubuwan hawan da za su yi jigilar maniyyata da sauransu, don yin Umurah da Sallah a Masallaci Mai Alfarma.”

Don haka Saeed ya yi kira ga maniyyata Umurah da suka fito daga jihohin yankin Gulf da su je su tantance matsayin rigakafin korona da suka yi a manhajar ‘Muqeem’ sa’o’i 72 kafin shiga Saudiyya.

Akwai buƙatar masu sha’awar zuwa Umurah su sauke manhajar Tawakkalna don gabatar da buƙatarsu da kuma samun izinin ‘permits’ da zai ba su damar gabatar da Umurah, gabatar da sallah a Masallacin Ka’aba, ziyartar Rawda Shareef da kabarin Annabi (SAW) da sauransu.

A baya-bayan nan Ma’aikatar Hajji da Umurah ta ɗaga adadin waɗanda za su riƙa yin Umurah a yini zuwa mutum 70,000.

Ma’aikatar ta jaddada cewa kulli yaumi za ta riƙa barin maniyyata daga ciki da wajen Saudiyya su riƙa gabatar da Umurah amma bisa tsararrun dokokin da aka samar don kare lafiya da kuma yaƙi da yaɗuwar korona.

A cewar ma’aikatar, baya ga manhajar ‘Eatmarna’, maniyyata na iya neman izinin ‘permits’ don yin Umurah da ziyara da sauransu ta manhajar ‘Tawakkalna’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here