Hajj Reporters ta yabawa Kano, Katsina kan maidowa maniyyata kuɗaɗensu

0
353

Hajj Reporters (IHR), Ƙungiya mai zaman kan ta da ke kawo rahotanni kan Hajji da Ummara ta yabawa Hukumomin Jin Daɗin da Walwalar Alhazai na Jihohin Kano da Katsina bisa ƙoƙarin da su ka yi wajen maida wa maniyyatan Hajjin shekarar 2020 da 2021 kuɗaɗensu.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Malam Ibrahim Muhammed, ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, ƙungiyar ta nuna gamsuwa da tsarin da hukumomin biyu su ka bi wajen maida wa maniyyatan da kuɗaɗensu sakamakon rashin yin aikin Hajji na 2020 da 2021.

Idan za a iya tunawa, Hajj Reporters ta buƙaci bayanan yadda tsarin maida wa maniyyata kuɗaɗen da su ka biya na Hajjin 2020 da 2021 ya gudana daga wasu jihohi domin ƙarfafawa hukumomin wajen yin aiki da gaskiya da kuma marawa gwamnati mai ci baya kan ƙudurinta na yin aiki a zahiri game da tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.

A cewar Muhammad, “Duk da cewa Katsina da Kano ba su daga cikin rukunin farko na jerin jihohin da aka aikawa da wasiƙar neman bayanai, amma duk da haka sun baiwa mara ɗa kunya wajen aiwatar da shirin maida wa maniyyatan 2020 da 2021 da kuɗaɗensu a kan kari.

“Jihar Katsina ta soma ne da tantance maniyyatan da kuma abin da kowannensu ya biya daga kowace shiyya, matakin da ta ɗauka domin kauce wa samun akasi wajen biyan kuɗaɗen. Yayin da ita kuma Jihar Kano ta yi amfani da tsarin kafa kwamiti na musamman da ya haɗa da jami’an tsaro da ‘yan jarida da wakilan ƙananan hukumomi da suka sanya ido kan shirin maida kuɗaɗen.

“Abu na biyu shi ne, Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki, ya saki bayanai dangane da shirin maida kuɗaɗen a ranar 20 ga Agusta domin al’umma su shaida lamarin.

“Sannan Hukumar a jihar Katsina, ta aiwatar da nata shirin ta hanyar bayyana komai kama daga adadin maniyyatan da aka yi wa rajista dangane da Hajjin 2020 da na 2021 zuwa bada cikakken bayanin kuɗin da aka maida wa kowannensu a tsakanin rukuni guda uku, adadin waɗanda aka maida wa kuɗaɗensu tare da kafa kwamiti mabambanta waɗanda suka sanya ido da kuma haɗa rahoto kan yadda komai ya gudana.

IHR ta ce wannan halin nagarta da hukumomin suka nuna hakan zai ƙara musu samun yarda da amincewar jama’a musamman ma maniyyata, dangane da sha’anin Hajjin 2022 idan Allah ya kai mu.

IHR ta ce ta gamsu da yadda Shugaban Hukumar Alhazai na Katsina, Nuhu Kuki, ya aiwatar da shirin maida wa maniyyatan da kuɗaɗensu a tsakanin rukuni guda uku.

Ta ƙara da cewa Nuhu Kuki ya ce, hukumar ta maida kuɗaɗe N407,834,977 ga maniyyata 331 a rukunin farko, sannan miliyan N176 ga maniyyata 134 a rukuni na biyu, yayin da aka biya miliyan N77,330 ga maniyyata 63 a rukuni na uku.

Yayin da yake ƙarin haske game da ayyukansu, Nuhu Kuki ya ce maniyyata 2,721 ne hukumar ta yi wa rajista game da sha’anin Hajjin 2020/2021 wanda mutum 508 daga cikin wannan adadi suka buƙaci a maida musu kuɗaɗensu wanda a jimillance ya kama Naira miliyan 661.

“Ita kuwa Hukumar Alhazai ta Kano, ta soma maida wa maniyyata da kuɗaɗensu ne bayan da aka sanar da soke Hajjin 2021, sannan bayan haka ta riƙa bada bayanai kan yadda ayyukanta ke gudana lokaci-lokaci wanda ya shafi adadin maniyyatan da suka buƙaci a maida masu kuɗaɗensu, adadin waɗanda aka maida musu da kuɗaɗen nasu, dadin kuɗin da aka maida wa konwannensu, da kuma adadin maniyyatan da suka amince a ci gaba da ajiyar kuɗaɗensu don Hajji mai zuwa. Irin wannan aiki da gaskiya ya cancanci mu yi yabo a kansa,” in ji IHR.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here