Alhazai miliyan goma ne suka yi Ummara tun ƙaddamar da matakan kariya

0
385

Ma’aikatar Hajji da Umurah ta Saudiyya ta bada sanarwar cewa mahajjatan Umurah su milyan 10 ne suka yi nasarar gabatar da Umurah tun daga ranar 4 ga watan Oktoban bara, bayan da aka ƙaddamar da shirin “Safe Umrah” ta hanyar la’akari da matakan kariya daga kamuwa da cutar korona da kuma maido da lamurra sannu-sannu a masallatai biyu masu alfarma.

Kazalika, Ma’aikatar ta sanar da cewa an bayar da bisa sama da 12,000 tun bayan da Masarautar ta soma karɓar baƙi maniyyata daga wajen ƙasar a watan Oktoban bara.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da yin dukkan mai yiwuwa wajen ci gaba da kare lafiyar maniyyata da sauran masu ibada da masu ziyara a masallatan masu alfarma. Tare da yin kira ga jama’a da su zamo masu kare dukkanin dokokin da aka shimfiɗa don yaƙi da yaɗuwar cutar korona.

Jami’an Saudiyya na burin ganin adadin maniyyata da sauaransu da ake samu ya ƙaru zuwa miliyan 3.5 duk wata. A cewar Mataimakin Ministan Hajji da Umurah, Abdulfattah bin Sulaiman Mashat, kawo yanzu adadin maniyyatan da ake samu duk yini ya kai mutum 70,000.

Ya ƙara da cewa, yin cikakken rigakafin koro na daga ciki wajiban da tilas a cika su kafin samun shaidar izinin Umurah ga maniyyata, haka ma lamarin yake ga sauran mutanen da ke da sha’awar ziyartar Masallacin Ka’aba da Masallacin Annabi.

Ya ce ana bayar da shaidar izinin ne ta hanyar amfani da manhajar Tawakkalna. Kana ya ce, hukumomin lafiya na Saudiyya sun halasta yi wa al’ummar ƙasar rigakafin korona amma ga waɗanda suka haura shekara 12 ƙaɗai.

Hukumomin Saudiyya sun ce suna ci gaba da tantance ƙasashen da za a lamunce musu zuwa yin Umurah ta hanyar lura da irin cigaban da kowace ƙasa ke samu a fagen yaƙi da annobar korona.

Ma’aikatar ta ce ana shawartar baƙi na ƙasa da ƙasa da su tantance matsayin rigakafin korona da suka yi a manhajar Muqeem sa’o’i 72 kafin kama hanyar tafiya Saudiyya. Sannan cewa, maniyyata za su iya neman agaji a wajen Ma’aikatar Hajji da Umurah a keɓaɓɓun wurare da aka samar don hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here