Yadda Ma’aikatar kula da Masallatan Harami Guda Biyu ta ke yiwa alhazai masu nakasa hidima

0
235

Ma’aikatar kula da Masallatan Harami Guda Biyu ta ɗauki ingantattun matakai domin samar wa maniyyata nakasassu yanayi mai sukuni da walwala yayin gabatar da ibadu a Masallacin Makka.

Fadar Shugabancin Saudiyya ta samar da wasu tsare-tsare na musamman waɗanda za su taimaka wa maniyyata nakasassu wajen gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba a Masallacin.

Matakan da aka ɗauka ɗin sun haɗa da: keɓe wasu wurare a cikin Masallacin don amfanin nakasassu kaɗai;

Sai kuma zuba wadatattun ƙur’anai don amfanin nakasassu masu neman taimako game da ji ko gani;

Gabatar da tsarin fassara huɗubar Juma’a duk mako cikin yaren kurame don amfanin masu buƙatar hakan, da kuma fassara huɗubar cikin harsuna daban-daban;

Samar da keken guragu na zamani a harabar hawa na ɗaya na Masallacin don taimaka wa nakasassun wajen gabatar da Ɗawafi cikin sauƙi;

Sannan an ɗauki matakin fassara huɗubar Juma’a da yaren kurame wanda ake sanyawa a tashar Ƙur’an don amfanin masu fama da lalurar rashin ji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here