Ba a buƙatar izinin yin sallah a Masallacin Ma’aiki

0
4

Ma’aikatar Kula da Harkokin Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta sanar da cewa babu buƙatar a nemi izni ko ba da ranar da za a yi sallah a cikin Masallacin Annabi a Madina ta manhajar Eatmarna.

“A na neman izni ne kawai idan za a yi sallah a Rawdah ko ziyara zuwa kabarin Ma’aiki Mai Tsira da Aminci su Ƙara Tabbata a Gare shi. Nuna shaidar kariya daga cutar korona ta manhajar Tawakkalna ita ce kaɗai shaidar da za a nuna domin shiga da yin Sallah a Masallacin Ma’aiki,” in ji ma’aikatar.

Ta ƙara da cewa a na son a ga shaidar kariyar ta manhajar Tawakkalna ta nuna cewa mutum ya yi duka alluran rigakafin korona sau biyu ko kuma shaidar cewa mutum ya kamu da cutar amma ya warke ko kuma ya kammala kwanaki 14 bayan ya samu kariyar ta hanyar ɗaukar rigakafin korona sau ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here