Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Guda Biyu na Saudi Arebiya, wato Harami na Makka da Madinah ya bayyana cewa an ɗauki ma’aikata mata guda ɗari shida (600) domin yin aikace-aikace a masallatan.
Kafar yaɗa rahotanni ta Haramain ta rawaito cewa an ɗauki ma’aikatan ne domin yiwa alhazai mata hidima a masallacin Harami na Makka da na Madina.