Buhari ya taya Saudiya murnar cika shekara 91 da kafuwa

0
235

Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya miƙa saƙon taya murna a madadin Nijeriya ga Sarkin Saudiyya kuma Hadimin Masallatai biyu masu alfarma, Sarki Salman bin Abdulaziz al-Saud bisa bikin cikar ƙasar shekaru 91.

Haka kuma Buhari ya taya Yarima Mai jiran gado na Saudiya, Mohammed bin Salman murna bikin wanda a ka yi shi a ranar Alhamis.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta nuna Buhari na matuƙar martaba alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Saudiyya wacce ta danganci baiwa juna haɗin kai da taimakekeniya.

Shugaba Buhari ya ce, Nijeriya za ta ci gaba da ɗaukar ƙawancen da ke tsakaninta da Saudiyya da muhimmanci, tare da ba da tabbacin cewa haka zumuntar za ta ci gaba da kasancewa mai armashi ƙarƙashin shugabancin ƙasashen biyu.

Buhari ya ƙara da cewa, yana da yaƙinin ƙasashen biyu za su ci gaba da yauƙaƙa dangantakar da ke tsakaninsu na shekaru da dama masu zuwa don amfanin kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here