Mun shirya tarbar alhazan Ummara daga Iraqi- Saudiyya

0
1

Ministan riƙon ƙwarya na Hajji da Ummara na Saudi Arebiya, Dr. Issam Bin Saad Bin Saeed, ya ce Saudiyya za ta karɓi maniyyatan Hajji da na Umurah na ƙasar Iraƙi kowane lokaci cikin wannan shekara. Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa tare da Jakadan Iraƙi a Saudiyya, Dr. Abdul Sattar Al-Janabi, a ranar Litinin da ta gabata.

Yayin ganawar tasu, jami’an biyu sun tattauna kan batutuwa masu nasaba da sha’anin maniyyatan Hajji da Umurah daga Iraƙi, da kuma irin ayyukan hidima da Gwamnatin Saudiyya take yi wa maniyyata.

Ministan ya jaddada irin muhimmancin da gwamnatin Saudiyya ta bayar wajen kula da Masallacin Makka da Madina da sauran muhimman wurare haɗa da baƙi masu ziyarar masallatan daga sasaan duniya.

Ya ce, “Saudiya na zumuɗin ganin ta bada mafi kyawun kulawa ga maniyyata da masu ziyara domin ba su zarafin aiwatar da ibadunsu cikin sukuni.”

Haka nan, Dr. Issam ya yaba da irin haɗin kai da goyon bayan da ake samu tsakani hukumomin Saudiyya da na Iraƙi don tabbatar da maniyyatan Hajji da Umurah daga sassan Iraƙi sun gabatar da ibadunsu cikin walwala da kwanciyar hankali. Yana mai cewa, wannan ya sake tabbatar da irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

A nasa ɓangaren, jakadan Iraƙin ya jinjina wa Saudiyya bisa kyakkyawar kulawar da take bai wa maniyyata daga sassan duniya, musamman kuma maniyyatan Iraƙi, tare da addu’ar Allah Ya ƙara wa masarautar Saudiyya nasara da bunƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here