Saudiya za ta fara karɓar alhazan Ummara ba adadi

0
647

Ma’aikatar Hajji da Umurah ta Saudiyya ta ce, ta shirya karɓar maniyyata Umurah komai ya wansu ba tare da ƙayyade adadi ba wanda hakan ya yi daidai da tsarin da ma’aikatar ta shirya aiwatar kafin ɓullar annobar korona.

Da yake magana da kafar Al-Sharq Al-Awsat, mataimakin ministan Hajji da Umurah, Dr. Amr Al-Madah ya ce, “An kammala dukkan shirye-shiryen da ake buƙata don karɓar maniyyatan. Hakan ba wa ni abu ba ne mai wahala ba.”

Ya ƙara da cewa, “Ma’aikatar Hajji na da halin da za ta iya kula da alhazan Umurah kamar yadda aka bai wa kowace ƙasa kasonta kafin ɓullar annobar korona kuma za mu yi hakan ne ba tare da fuskantar wata wahala ba.”

A cewarsa, Ma’aikatar tana ƙoƙarin inganta manhajar ‘Shyaar’ da ta ‘Itmarna’ ta yadda alhazan Hajji da Umurah za su iya aiwatar da komai cikin lokaci ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Ya ci gaba da cewa, an samu nasara wajen yin amfani da manhajar hajji da aka samar yayin aikin hajjin da ya gabata.

Yana mai cewa, manhajar na tattarawa tare da adana dukkan bayanan mahajjata ba tare da barin komai ba. Ya ce da taimakon wannan manhajar za a iya kula da ɗaukacin mahajjata yadda ya kamata ba tare da wata mishkila ba.

Haka nan, ya ce nan gaba za a samar da katin amfani da manhajar Shyaar don amfanin alhazan Umurah don samun sauƙin sha’ni.

Sai dai, mataimakin ministan ya ce a halin yanzu, babu manhajar ‘Shyaar’ ga baƙi waɗanda suke ɗauke da katin ‘visa’ daga kamfanoni masu shirya tafiya Umurah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here