Korona: Saudiya ta ƙara sassauta matakan tafiye-tafiye

0
3

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa, waɗanda suka yi rigakafin korona sau guda ko na dukkan adadin da ya kamata a cikin ƙasar, za a cire su daga tsarin killacewa.

Wata majiya daga Ma’aikatar Kula da Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ce ta bayyana hakan.

Majiyar ta ce, duba da irin ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ta yi kan sha’anin yaƙi da cutar korona, da kuma bayanan da hukumomin lafiya suka gabatar, hakan ya sa a ka ɗauki matakin barin baƙi daga ƙasashen waje su shigo ƙasar ba tare da killacewa ba saɓanin yadda lamarin yake a baya.

A cewar majiyar, jami’oin ƙasar da takwarorinsu haɗa da malaman makarantun gwamnati a faɗain ƙasar da sauransu, za su ci gajiyar wannan dama muddin za su kiyaye dokokin da aka gindaya.

Kazalika, majiyar ta ce sassaucin ya haɗa har da janye dokar haramcin tafiye-tafiyen ‘yan ƙasa da shekara 18 daga Saudiyya zuwa Bahrain muddin za a kiyaye dokokin da suka kamata.

Haka nan, majiyar ta nuna buƙatar da ke akwai na kowa ya kiyaye ƙa’idojin kariya daga kamuwa da korona da kuma yaɗa ta.

Majiyar ta ƙara da cewa, hukumomin lafiya ba za su yi sake ba, za su ci gaba da sanya ido kan yadda jama’a ke biyayya wajen kiyaye dokokin da aka shimfiɗa game da tafiye-tafiye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here